Taimakon Musulmin Jamus ga 'yan gudun hijra
Wani sabon bincike ya nuna cewa kimanin rabin Musulmin kasar Jamus na taimakawa 'yan gudun hijra a kasar
A wani rahoto da Jaridar Spiegel ta kasar Jamus ta fitar a jiya Laraba, ta ce bisa wani sabon bincike da cibiyar Britslman ta gudanar na nuni da cewa Al'ummar musulmin kasar su fi saura mabiya Addinai har ma da kiristoci wajen taimakawa 'yan gudun hijraa kasar.
Kashi 44% na musulmin kasar sun taimakawa 'yan gudun hijra a shekarar 2016 da ta gabata, alhaki alkaluma sun nuna cewa a shekaru 2013 da kuma 2014 kashi daya cikin hudu ne na musulmin kasar ke taimakon 'yan gudun hijra.
Wannan taimako da Al'ummar Musulmin Jamus ke yi ga 'yan gudun hijra na zuwa ne a yayin da mafi yawa daga cikin kasashen Turai ke samar da dokoki masu tsauri na hana shigar 'yan hijrar cikin kasashen su.