Zaizayar Kasa ta yi sanadiyar mutuwar Mutane 92 a kasar Colombia
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19036-zaizayar_kasa_ta_yi_sanadiyar_mutuwar_mutane_92_a_kasar_colombia
Sanadiyar zaizayar kasa a kudancin Colombia, akalla Mutane 92 ne suka rasa rayukansu.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Apr 01, 2017 13:30 UTC
  • Zaizayar Kasa ta yi sanadiyar mutuwar Mutane 92 a kasar Colombia

Sanadiyar zaizayar kasa a kudancin Colombia, akalla Mutane 92 ne suka rasa rayukansu.

Magabatan kasar Colombia sun sanar a wannan Assabar cewa zaizayar kasa da ta biyo bayan ambaliyar ruwa a Kogin Muwakowa ta yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 92 tare kuma da jikkata wasu 180 na daban.

A cewar Carlos Ivan Marquez Daraktan cibiyar dake sanya ido kan yiyuwar aukuwar bala'i a kasar Colombia ya bayyana cewa zaizayar kasar ta auku ne a tsakiyar daren juma'a, sannan kun baya ga hasarar rayukan da aka samu gidaje da dama na bakin kogi sun rushe.

Har ila yau, Rahoton ya ce daruruwan Mutane sun bace sanadiyar wannan masiba, kuma yanzu haka an kafa gungu gungu da dama da suka hada da Sojoji,'yan sanda da mutanan gari domin neman wadanda suka bace da kuma taimakawa wadanda suka ji rauni.