Colombiya : Sama Da Mutane 200 Suka Mutu A Zaftarewar Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19058-colombiya_sama_da_mutane_200_suka_mutu_a_zaftarewar_kasa
An shiga zamen makoki a Columbiya bayan mumunar zaftarewar kasa da kawo yanzu tayi sanadin mutuwar mutane sam da 200 da kuma wasu daririwa da suka raunana.
(last modified 2018-08-22T06:59:54+00:00 )
Apr 02, 2017 06:05 UTC
  • Colombiya : Sama Da Mutane 200 Suka Mutu A Zaftarewar Kasa

An shiga zamen makoki a Columbiya bayan mumunar zaftarewar kasa da kawo yanzu tayi sanadin mutuwar mutane sam da 200 da kuma wasu daririwa da suka raunana.

Wannan dai shi ne iftila'i mafi muni da kasar ta fuskanta bayan makamanciyyarta a shekara 2010.

Shugaban kasar Colombiya Juan Manuel Santosm, ya sanar a Jiya Asabar cewa, an kafa dokar ta baci a Mocoa, babban birnin Putumayo dake kudu maso yammacin kasar, bayan da aka samu ibtila'in.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sa wasu koguna 3 dake yankin suka tumbatse  inda ambaliyar ruwan tayi awon gaba da gidaje, gadoji da ababan hawa masu yawan gaske.

A kalla birane 17 ne wannan bala'in ya shafa, kuma tuni shugaba Santos na kasar ya kai ziyara inda lamarin ya afku, sannan ya bada umarnin tura jami'an sojoji, 'yan sanda da sojin sama domin agazawa jami'an aikin ceto a yankin.