Colombiya : Adadin Mutanen Da Zaftarewar Kasa Ya Kashe Ya Karu
Apr 03, 2017 06:30 UTC
Shugaban Columbiya, Juan Manuel Santos, ya sanar da cewa addadin 'yan kasar da zaftarewar kasa ya yi ajalinsu na dada karuwa, inda kawo yanzu addadinsu ya kai 254.
Daga cikin dai wadanda lamarin ya rusa dasu da akwai yara 43, kamar yadda shugaba Santos, ya sanar a shaffinsa na Twitter,
Shugaba Santos ya kuma nuna alhininsa ga iyalen mutanen da iftila'in ya rusa dasu.
Bayanai daga kasar dai sun nuna cewa mai yiwa addadin mutanen da lamarin ya rusa dasu ya zarta hakan.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a birnin Mocoa ya sa wasu koguna uku a yankin suka tumbatse inda ambaliyar ruwan tayi awon gaba da gidaje, gadoji da ababan hawa masu yawan gaske.