Amurka Ta Yi Lugudan Makami Mai Linzami A Syria
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19202-amurka_ta_yi_lugudan_makami_mai_linzami_a_syria
Amurka ta sanar da kai wasu jerin hare-hare kan sansanin sojin saman Shayrat na Syria a cikin daren jiya Alhamis.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Apr 07, 2017 04:02 UTC

Amurka ta sanar da kai wasu jerin hare-hare kan sansanin sojin saman Shayrat na Syria a cikin daren jiya Alhamis.

An dai kai jerin hare-hare ne tun daga wasu jiragen ruwan Amurka dake gabashin tekun Bahar Rum.

Makamai masu linzami guda 59 ne aka harba kan sansanin sojin na Shayrat, wanda aka tarwatsa jiragen saman soji da hanyoyin jirgi da kuma wuraren shan mai a cewar wata majiyar gwamnatin Amurka.

Wannan dai a cewar  ma'aikatar tsaron Amurkar maida martani ne kan zargin da ita da kawayenta sukewa gwamnatin Bashar-Al Assad na kai hari da makamin iskar gas mai guba samfarin ''Sarin'' kan al'ummarsa.

Tuni dai gwamnatin Syria ta tabbatar da kai mata harin, tana mai cewa na tsokana ne, wanda ta ce ya hadasa hasara mai yawa saidai ba tare da yin karin haske ba.

Mutane 86 ne da suka hada da yara 27 suka rasa rayukansu a harin na ranar Talata a kauyen Khan Cheikhoun dake yankin Iblid a arewa maso yammacin Syria.

Amurka da kawayenta dai sun ki amuncewa da ikirarin gwamnatin Syria na nisanta kan ta da kai harin na makami mai guba.