Sakamakon Karshe NA Zaben Raba Gardamar Kasar Turkia
Bayan yakin neman zabe na watanni masu yawa daga karshe an gudanar da zaman raba gardama kan gabatar da sauye sauye a cikin kundin tsaron mulkin kasar Turkia a ranar Lahadin da ta gabata. Sannan sakamakon ya nuna cewa ra'ayin amincewa da hakan ya sami rinjaye da dan kadan.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa an kammala kidayar kuri'un da aka kada a akwatunan zabe 167,000 daga mazabu dubu 140 a misalin karfe 5 na yamma, inda sakamakon ya nuna cewa ra'ayin amincewa da sauya kundin tsarin mulkin ya sami rinjaye da dan kadan kan ra'ayin da bai amince ba, wato rinjaye na bai fi kashi 2.6 ba.
Kafafen yada labarai sun bayyana cewa yawan fitowan wadanda suka cancanci kada kuri'a a wannan zaben ya kai kashi 86 % wanda shi ne mutum miliyon 56,588,505. Majiyar ma'aikatar cikin gida na kasar Turkia ta bayyana cewa idan sakamakon zaben na 16 ga watan Afrilu ya sami amincewa ta karshe za'a sauya dokoki 18 a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan da shekara ta 2019 lokacinda za'a fara aiwatar da su. Muhimman abubuwan da sauyin zai shafa a kundin tsarin mulkin dai sun hada da bawa shugaban kasa iko mai yawa, shafe kujerar Priminister da kuma takaida karfin majalisar dokokin kasar a cikin harkokin siyasa na ci ki da wajen kasar.
Sakamakon wannan zaben ya nuna cewa, duk tarade karamin rinjayen da ra'ayin amincewa ya samu, kasancewa masu adawa da shi suna da yawa, wannan ya nuna cewa aiwatar da sabbin dokokin zai fuskanci adawa mai tsanani idan an fara aiwatar da su.
Ya zuwa yanzu dai babban jam'iyyar adawar kasar ta Turkia "Republican People's Party" ta yi watsi da sakamakon zaben ta kuma bukaci a kidayar kashi 60% na kuri'un da aka kasa a wannan zaben.
Yankun Gabas da kuma kudu maso gabcin kasra ne suka fi kada kuri'un rashin amincewa da sauya kundin tsarin mulkin wanda ya nuna cewa shugaba Rajab Tayyeed Urdogan yana da manya manyan matsalolin da zai fuskanta nan gaba.
Daga karshe masu nazarin harkokin siyasar kasar Turkia da kuma irin halin da yankin gabas ta tsakiya take cikin suna ganin za'a sami sauye sauye masu yawa a matsayin kasar ta Turkia dangane da rikicin kasar Syria da kuma dangantakarta da kasashen tarayyar Turai.