Amurka : Dan Bindiga Ya Hallaka Mutum Uku A California
Wani dan bindiga a Amurka ya hallaka mutum uku tare da raunana wasu hudu a birnin Fresno dake jihar California.
Mutumin dan shekara 39 mai suna Kori Ali Muhammad wanda kuma akewa lakabi da "Black Jesus" ya yi ta kabbara da larabci a lokacin da yake mika kansa ga 'yan sanda.
Hukumar 'yan sanda a yankin ta ce mutumin wanda bakar fata ne ya wallafa a shafinsa na facebook da kuma lokacin da 'yan sanda suka kama shi cewa yana kyammar fararen fata da kuma gwamnatin Amurkar.
Saidai da yake bayyani ga manema labarai kwamandan 'yan sanda yankin Fresno Jerry ya ce kisan da mutumin ya yi ba yada alaka da ta'addanci, amman na wariyar launin fata ne.
Mahaifin maharin dai ya shaidawa mujjalar Los Angeles Times cewa dan na sa ya shaida masa cewa zai shiga wani yaki dake tafe na tsakanin bakake da fararen fata.
Dama kafin hakan maharin Ali Muhammad wanda 'yan sanda ke farautarsa ya hallaka wani jami'in 'yan sanda na yankin a makon da ya gabata.