An Fara Gagarumin Atisayen Sojin Tsakanin Amurka Da Wasu Kasashen Afirka
A jiya Juma'a ce aka fara gudanar da wani gagarumin atisayen sojin da aka ba shi sunan "African Lion" tsakanin sojojin ruwan Amurka da wasu daruruwan sojojin da suka fito daga kasashe 11 na duniya a kasar Moroko.
Kafar watsa labaran Moroccon News ya bayyana cewar a jiya Juma'a ce aka fara wannan atisayen wanda ake ganinsa a matsayin mafi girman atisayen soji da aka taba gudanarwa a nahiyar Afirkan wanda zai kumshi sojoji daga kasashen Amurka, Moroko, Faransa, Jamus, Birtaniyya, Spain, Kanada, Mali, Mauritaniya, Senegal da kuma Tunusiya.
Manufar wannan atisayen dai da ake gudanar da shi kowace shekara tun daga shekara ta 2007 a kasar Morokon ita ce ba wa sojojin Amurka da na Turai wata dama ta horo da samun kwarewa kan wasu yanayi da suka saba wa wanda suke ciki kamar yadda kuma ya kan ba wa sojojin kasashen Afirkan musamman na Moroko samun horaswa kan wasu dabarun yaki daga wajen sojojin Amurka da na Turai din.
Za a ci gaba da wannan atisayen dai har zuwa ranar 28 ga watan Aprilun nan da muke ciki.