Rasha Ta Musanta Zargin Amurka Kan Aikewa Da Makamai Zuwa Afganistan
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19804-rasha_ta_musanta_zargin_amurka_kan_aikewa_da_makamai_zuwa_afganistan
Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya yi watsi da zargin mahukuntan Amurka kan kasarsa na cewa: Rasha ce ke aikewa kungiyar Taliban da makamai, tare da bayyana zargin da cewa karya ce tsagwaronta.
(last modified 2018-08-22T07:00:01+00:00 )
Apr 25, 2017 10:16 UTC
  • Rasha Ta Musanta Zargin Amurka Kan Aikewa Da Makamai Zuwa Afganistan

Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya yi watsi da zargin mahukuntan Amurka kan kasarsa na cewa: Rasha ce ke aikewa kungiyar Taliban da makamai, tare da bayyana zargin da cewa karya ce tsagwaronta.

A ganawarsa da manema labarai a yau Talata: Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya yi furuci da cewa zargin Amurka na cewa Rasha tana aikewa kungiyar Taliban na kasar Afganistan da makamai, zargi ne maras tushe kuma karya ce tsagwaronta.

Kafin nan Janar John Nicholson babban kwamandan rundunar mamayar Amurka a Afganistan ya yi zargin cewa; Kasar Rasha ce ke aikewa mayakan kungiyar Taliban da makamai. Har ila yau sakataren tsaron kasar Amurka James Mattis ya yi da'awar cewa kasarsa zata dauki matakan kalubalantar gwamnatin Rasha kan zagon kasa da take yi wa dakarun kawance a Afganintan.

Kasar Amurka tana da sojoji kimanin 10,000 da ta jibge a Afganistan baya ga dakarun kawance na kungiyar tsaro ta NATO da suke kasar amma sun kasa shawo kan matsalolin tsaro da suke ci gaba da addabar kasar ta Afganistan, inda ko a ranar Juma'ar da ta gabata sai da wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Taliban suka kai farmaki kan Masallacin Juma'ar rundunar sojin Afganistan da ke kusa da Mazare-Sharif a lardin Balkh, inda suka kashe mutane kimanin 150 tare da jikkatan wasu fiye da 80 na daban.