Paparoma Francis Ya Fara Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19902-paparoma_francis_ya_fara_gudanar_da_ziyarar_aiki_a_kasar_masar
Shugaban darikar Katolika ta mabiya addinin Kirista ta duniya Paparoma Francis ya fara gudanar da ziyarar aiki ta kwanakin biyu a kasar Masar, inda ya isa birnin Alkahira fadar mulkin kasar a jiya Juma'a.
(last modified 2018-08-22T07:00:02+00:00 )
Apr 29, 2017 00:50 UTC
  • Paparoma Francis Ya Fara Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar Masar

Shugaban darikar Katolika ta mabiya addinin Kirista ta duniya Paparoma Francis ya fara gudanar da ziyarar aiki ta kwanakin biyu a kasar Masar, inda ya isa birnin Alkahira fadar mulkin kasar a jiya Juma'a.

Ziyarar aikin da Paparoma Francis shugaban darikar katolika ta mabiya addinin Kirista ta duniya ya fara a kasar Masar tana matsayin ci gaba da karfafa matakin tattaunawa ne tsakanin mabiya addinin Musulunci da na kirista da aka fara a shekarar da ta gabata a birnin Rom na kasar Italiya tsakanin mabiya addinan biyu.

A shekarar tada gabata shugaban jami'ar Azhar Sheikh Ahmad Tayyib ya kai ziyarar aiki zuwa fadar Vatican ta mabiya darikar katolika, inda ya samu kyakkyawar tarba daga Paparoma Francis shugaban darikar katolika ta mabiya addinin kirista ta duniya lamarin da ya kawo karshen rashin fahimtar juna na tsawon shekaru biyar tsakanin Jami'ar Azhar da fadar ta Vatican. Sabanin mahanga da rashin jituwa tsakanin Jami'ar Azhar ta Masar da fadar Vatican ta kunno kai ne sakamakon furuncin batanci da Paparoma Benedic na 16 tsohon shugaban darikar katolika ta duniya ya yi ne kan addinin Musulunci. Haka nan ziyarar aikin da Paparoma Francis ya kai zuwa Masar a daidai wannan lokaci yana da muhimmanci musamman ganin a cikin 'yan kwanakin baya-bayan nan ne 'yan ta'addan kungiyar Da'ish suka kai wasu jerin munanan hare-haren wuce gona da iri kan majami'un mabiya addinin kirista a kasar ta Masar da nufin janyo rashin jituwa tsakanin mabiya addinin Musulunci da na kirista.  

Hakika matakan da Paparoma Francis yake dauka na neman wanzar da zaman lafiya da sulhu a tsakanin mabiya addinai musamman tsakanin mabiya addinin kirista da na Musulunci, matakai ne masu muhimmanci kuma abin yabo alal misali a daidai lokacin da wasu kafafen watsa labaran kasashen yamma da gwamnatocinsu ga misali shugaban kasar Amurka Donald Trump ke kokarin daidaita tsakanin addinin Musulunci da akidar ta'addanci, Paparoma Francis ya fito fili ya karyata wannan da'awa maras tushe, inda ko a cikin watan Fabrairun wannan shekara ta 2017 ya fito ya karyata da'awar cewa akwai samuwar wani abu mai suna "Ta'addan Musulunci". Kamar yadda Paparoma Francis ya yi fice a fagen jaddada samun fahimtar juna da sulhu a tsakanin mabiya addinai na duniya tare da fayyace samuwar 'yan ta'adda masu dauke da akidar wuce gona da iri a kowane addini.

Tabbas bullar ayyukan ta'addancin wasu kungiyoyin 'yan ta'adda masu dauke da akidar kafirta musulmi musamman 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish a wasu kasashen yammcin Turai da Amurka hakan ya taimaka wajen karfafa gwiwar masu kiyayya da addinin Musulunci tare da kara zaburar da su kan yada farafagandar kiyayya da munanta addinin Musulunci da musulmi, kuma sakamakon haka ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya karbi ragamar shugabancin kokarin bakanta addinin Musulunci tare da yada akidar kyamatar musulmi a kasar Amurka. Kamar yadda a lokacin yakin neman zabensa ya sanar da cewa idan har ya dare kan karagar shugabancin Amurka zai dauki matakin hana musulmi hakkin shiga cikin kasar a karkashin shirinsa na yaki da ta'addanci, kuma a halin yanzu haka yana ta kokarin ganin ya cimma wannan bakar aniyar tasa. Sakamakon haka matakin da Paparoma Francis ke dauka na kokarin samar da wani fagen tattaunawa a tsakanin mabiya addinai musamman musulmi da kirista lamari ne da zai yi gagarumin tasiri wajen wayar da kan al'ummar duniya musamman na kasashen yammacin Turai da Amurka kan matsayin addini a fagen rayuwar bil-Adama da irin gagarumar rawar da yake takawa wajen wanzar da zaman lafiya da sulhu da kuma habaka ci gaban rayuwa cikin tsari da daidaito.