Lupen Ta Zargi Abokin Hamayarta Da Kasancewa Tare Da Musulman Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20010-lupen_ta_zargi_abokin_hamayarta_da_kasancewa_tare_da_musulman_kasar
Yar takarar shugaban kasa a kadar Faransa Maria Le Pen ta zargi abokin hamayarta Emmanuel Macron da hada kai tare da musulman kasar faransa.
(last modified 2018-08-22T07:00:03+00:00 )
May 02, 2017 10:29 UTC
  • Lupen Ta Zargi Abokin Hamayarta Da Kasancewa Tare Da Musulman Kasar

Yar takarar shugaban kasa a kadar Faransa Maria Le Pen ta zargi abokin hamayarta Emmanuel Macron da hada kai tare da musulman kasar faransa.

Tashar Television ta RTL ta nakalto Lepen tana fadar haka a lokacin yakin neman zabe a yau Talata, ta kuma kara da cewa macron yana hada kai tare da gamayyar kungiyoyin musulmi ta UOIF a zaben da za'a gudanar a ranar 7 ga watan mayun da muke ciki.

Gamayyar kungiyoyin musulmi ta kasar Faransa ta karyata wannan labarin ta kuma kara da cewa babu wata dangantaka ta musamman da take da Emmanuel Macron, sai dai tana kira ga musulmi masu zabe a kasar faransa su kadawa Emmanuel Macron Kuri'unsu a ranar zabe. Wannan kuma don abinda ita Lepen take fada na cewa zata takurawa musulmi idan ta ci zaben shugaban kasa mai zuwa.

Akwai kungiyoyin musulmi da masallatai kimani 250 karkashin laimar kungiyar ta UOIF.