Fashewar Wani Abu A Birnin Kabul Na Kasar Afganistan
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20022-fashewar_wani_abu_a_birnin_kabul_na_kasar_afganistan
Karan fashewar wani Abu ya girgiza birnin Kabul fadar milkin kasar Afganistan a safiyar yau laraba.
(last modified 2018-08-22T07:00:03+00:00 )
May 03, 2017 01:13 UTC
  • Fashewar Wani Abu A Birnin Kabul Na Kasar Afganistan

Karan fashewar wani Abu ya girgiza birnin Kabul fadar milkin kasar Afganistan a safiyar yau laraba.

Fashewar abun ya faru ne a babbar hanyar Abdulhaq dake yanki na 9, inda Ofishin Jakadancin kasar Amurka yake, kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran  ya ce an ji karan alamar hatsari da kuma kukan Motoci agaji na Ofishin jakadancin kasar Amurka.

Ya zuwa yanzu dai babu wani cikekkenbayyani dangane da asarar da wannan hari ya janyo.

A Daren litinin da ta gabata, Dakarun kasar Afganistan sun sanar da dakile wani harin ta'addanci a kusa da Asibitin Jamhoriya dake birnin Kabul, a makun da ya gabata ma, birnin na kabul ya fuskanci hare-haren ta'addanci da dama, lamarin da yayi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar Mutane da dama.

Kwanaki biyu da suka gabata Ofishin Jakadancin kasar Amurka dake birnin Kabul ya gargadi 'yan kasarsa da su guji bulaguro zuwa kasar ta Afganistan saboda kaucewa hare-haren masu adawa da Gwamnatin kasar.