Marine Le Pen Ta Taya Emmanuel Macron Murnar Lashe Zaben Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20178-marine_le_pen_ta_taya_emmanuel_macron_murnar_lashe_zaben_faransa
'Yar takarar shugabancin kasar Faransa Marine Le Pen wadda ta sha kayi a zagaye na biyu, ta taya abokin karawar nata Emmanuel Macron murnar lashe zaben.
(last modified 2018-08-22T11:30:04+00:00 )
May 08, 2017 07:30 UTC

'Yar takarar shugabancin kasar Faransa Marine Le Pen wadda ta sha kayi a zagaye na biyu, ta taya abokin karawar nata Emmanuel Macron murnar lashe zaben.

Rahotanni daga kasar Faransa sun ce magoya bayan Macron sun kwana suna ta murna a dukkanin sassa na kasar, yayin da shugabannin kasashen duniya suke ci gaba da aikewa da sakon taya murna ga Emmanuel Macron wanda ya samu nasarar lashe zaben.

Emmanuel Macron dan shekaru 39 da haihuwa kuma mai matsakaicin ra'ayi, ya samu nasarar lashe zaben ne da kashi 65.1 cikin dari na dukkanin kuri'un da aka kada, inda abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen mai tsatsauran ra'ayin 'yan mazana ta samu kashi 34.9 cikin dari na kuri'un, wadda ta taya shi murna tun kafin sanar da sakamakon karsshe, ta kuma sanar da cewa jam'iyyarta za ta kasance babbar jam'iyyar adawa a kasar ta Faransa a halin yanzu.

A ranar Lahadi mai zuwa ce Farncois Hollande shugaban Faransa mai barin gado, wanda kuma ya goyi bayan Emmanuel Macron, zai mika mulki ga zababben shugaban kasar ta Faransa.