Kyamar Musulunci Ta Karu Da Kashi 57 Cikin Dari A Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20256-kyamar_musulunci_ta_karu_da_kashi_57_cikin_dari_a_amurka
Babbar cibiyar musulmi a kasar Amurka ta fitar da wani rahoto da ke nuni da cewa kyamar musulmi ta karu a kasar a cikin wannan shekara.
(last modified 2018-08-22T07:00:05+00:00 )
May 10, 2017 14:53 UTC
  • Kyamar Musulunci Ta Karu Da Kashi 57 Cikin Dari A Amurka

Babbar cibiyar musulmi a kasar Amurka ta fitar da wani rahoto da ke nuni da cewa kyamar musulmi ta karu a kasar a cikin wannan shekara.

Kamfanin dillancin labaran Reauters ya bayar da rahoton cewa, a cikin rahoton da babbar cibiyar musulmin kasar Amurka ta fitar, ta tabbatar da cewa a shekara da ta gabata, an aikata laifuka na cin zarafin musulmi tare da nuna musu kyama har sau 2213, a cikin shekara ta 2016.

Rahoton ya ce idan aka kwatanta wadannan ayyuka na shekarar da ta gabata, da kuma ayyukan cin zarafi da nuna kyama ga musulmia cikin wannan shekara a cikin kasar Amurka, ayyukan sun karu da kashi 56 cikin dari, duk kuwa da cewa ana cikin rabin farko na shekarar bana.

Cibiyar musulmin Amurka ta ce wannan yana faruwa ne sakamakon irin matakan da sabbin mahukuntan kasar Amurka suke dauka a karkashin salon siyasar Donald Trump ta kin jinin musulmi, inda hatta jami’an hukumar tsaro ta FBI na suna tsananta ayyukansu a halin yanzu a kan musulmi a kasar.