Macron Ya Zama Shugaban Kasar Faransa A Hukumance
Shugaban majalisar kare kundin tsaron mulkin kasar Faransa, a jiya Alhamis ya bada sanrawan cewa Emmanuel Macron ne zabebben shugaban kasar Faransa.
Tashar television ta France 24 ta bayyana cewa wannan matakin yana da muhimmanci a tsarin shugabanci na kasar Faransa, kuma wannan sanarwan ta tabbatar da cewa a duk lokacinda wa'adin mulkin shugaban kasa mai ci, Fransua Holanda ya cika Macron ne zai maye gurbinsa.
Da misalin karfe 12 dare na ranar 14 ga watan Mayu da muke cikin ne wa'adin shugabancin shugaba Fransua Holanda zai ciki, kuma tun lokacinne Macron zai karbi ragamar shugabancin kasar Faransa har na tsawon shekaru 5 .
Labarin ya kara da cewa majalisar kare kundin tsarin mulkin ta tabbatar da cewa an gudanar da zaben shugaban kasa na kasar ta Faransa a ranar 7 ga watan mayu da muke cikin, cikin tsabta da kuma adalci.