Babban Bankin Birtaniya Ya Nuna Damuwa Kan Yanayin Tattalin Arzkin Kasar
Babban bankin kasar Birtaniya ya nuna damuwa matuka dangane da halin da tattalin arzikin kasar yake ciki.
A cikin rahoton da babban bankin na kasar Birtaniya ya fitar a jiya ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar yana samun koma baya, inda a cikin wattani 6 na farkon wannan shekara zai ja ba da kashi 1.9 cikin dari.
A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jiya a London, gwamnan babban bankin kasar Birtaniya Mark Carney ya bayyana cewa, tsadar rayuwa ta karu daga kashi 2.4 zuwa kashi 2.7 cikin dari, wanda hakan ke nuni da cewa albashin da ma'aikata suke karba a Birtaniya ba daidai yake da bukatunsu na yau da kullum.
Masana tattalin arziki a kasar ta Birtaniya dai na bayyana matsalar faduwar kudin pound da kuma wasu matsalolin tattalin arziki da kasar ke fuskanta, da cewa yana da nasaba ne da ficewar kasar daga kungiyar tarayyar turai