Koriya Ta Arewa Ta Sake Gwajin Makami Mai Linzami
May 22, 2017 08:49 UTC
Koriya ta Arewa ta sake gwajin wani makamai mai linzami mai cin matsakaicin zango duk da tsauraren takunkuman da Amurka da MDD ke kakaba mata akan hakan.
kanfanin dilancin labaren KCNA shugaba Kim Jong-Un ne ya jagoranci harba makamin , wanda shi ne karo na 11 data harba a cikin wannan shekara.
Rundinar sojin makofciyar kasar wato Koriya ta Kudu ta ce makamin ya ci kilomita 500 kafin ya fado a tekun Japon.
Tuni dai mahukuntan Washigton da Seyul da Tokiyo sukayi Allah wadai da sabon gwajin tare da kiran wani taron gaggawa na kwamitin tsaron MDD a gobe Talata.