Martanin MDD Kan Furucin Trump Dangane Da Yarjejeniyar Dumamar Yanayi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20882-martanin_mdd_kan_furucin_trump_dangane_da_yarjejeniyar_dumamar_yanayi
Babban sakataren majalisar dinkin duniya António Guterres ya mayar da martani a kan furucin shugaban Amurka Donald da ke neman a yi watsi da yarjejeniyar birnin Paris kan dumamar yanayi.
(last modified 2018-08-22T07:00:11+00:00 )
May 31, 2017 07:43 UTC
  • Martanin MDD Kan Furucin Trump Dangane Da Yarjejeniyar Dumamar Yanayi

Babban sakataren majalisar dinkin duniya António Guterres ya mayar da martani a kan furucin shugaban Amurka Donald da ke neman a yi watsi da yarjejeniyar birnin Paris kan dumamar yanayi.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a jiya a Majalisar dinkin duniya, António Guterres ya ce ya kamata sauran kasashen duniya su aiki da yarjejeniyar da aka cimmawa a birnin Paris kan dumamar yanayi, ba tare da yin la'akari da wadanda suka karya wannan yarjejeniya ba, yana mai ishara da gwamnatin Amurka.

Ya ce abin da wannan yarjejeniya ta kunsa aiwatar da hakan shi ne kadai zai taimaka wajen rage dumamar yanayi a duniya, wanda yake haifar da matsaloli masu tarin yawa a halin yanzu ga duniya.

Yarjejeniyar wadda dukkanin kasashen duniya suka sanya hannua  kanta a cikin watan Disamban 2015 a birnin Paris na kasar Faransa, ta kunshi matakai da dama, da suka hada da daukar matakin rage ayyukan da suke jawo dumamar yanayi a duniya, da kuma biyan kudade daga manyan kasashe da suke da manyan kamfanoni domin gudanar da wannan aiki, amma bayan zuwa Donald Trump a fadar white house, yasa kafa ya yi fatali da wannan yarjejeniya, inda ya ce yin aiki da wannan yarjejeniya zai cutar da harkokin kamfanonin Amurka.