An Galgadi Amurka Kan Sake Kakabawa Iran Takunkumi
Tsohon Ministan Harakokin Wajen Amurka Ya Galgadi Gwamnatin Kasar da sake kakabawa Iran sabon Takunkumi
Jean Kery ya bayyana cewa kakabawa jumhoriyar musulinci ta Iran sabon takunkumi wani sakon ne ga Al'ummar Iran cewa jerjrjjeniyar da aka cimma na nukuliyar kasar a shekarar 2015 ba shi da wani amfani.
A watan da ya gabata ne kwamitin dake kula da harakokin waje na Majalisar Datijan kasar Amurka ya kada kuri'ar amincewa na baiwa Shugaban kasar damar kakabawa Jumhoriyar Musulinci ta Iran sabin takunkumi.
Tsohon Ministan harakokin wajen Amurka ya bayyana fatansa ga Shugaba Trump da ya saurari irin sukar da ake yi wa siyasar Gwamnatin kasar.
A gobe Laraba ne ake sa ran za a gabartawa Majalisar Datijan kasar Amurka wani sabon shiri na kakabawa Kasar Iran sabin takunkumi kan da'awar cewa tana gudanar da wasu aiyuka da suka kawo cikas a tsaro da kuma zaman lafiyar gabas ta tsakiya.