James Mattis: Rundunar Sojin Amurka Ta Samu Koma Baya
Sakataren tsaron Amurka James Mattis ya bayyana cewa, rundunar sojin kasar ta samu koma baya idan aka kwatanta irin shirin da take da shi a shekarun baya.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoto daga birnin Washington cewa, a jiya sakataren tsaron Amurka James Mattis ya bayyana gaban kwamitin kula da ayyukan sojojin Amurka na majalisar dokokin kasar domin amsa tambayoyi kan wasu batutuwa da suka shafi kasafin kudin shekara ta 2018 da aka warewa bangaren tsaro.
A lokacin da yake amsa tambayoyin mambobin kwamitin, Mattis ya bayyana kaduwarsa matuka kan abin da ya kira gagarumin koma baya da rundunar sojin Amurka ta samu ta fuskoki da dama a cikin shekarun baya-bayan nan.
ma'aikatar Pentagon ta bukaci a ware dala biliyan 639 ga ayyukan tsaro a 2018, inda biliyan 574 za su tafi a bangaren ayyuka na yau da kullum a bangaren tsaro, dala biliyan 65 kuma za su tafi a yake-yaken da Amurka take yi a duniya.