Adawar Sanatocin Amurka Dangane Da Sayarwa Saudiya Makamai
Wani Sanata na Jam'iyar Republicain ya bayyana cewa ya zama wajibi Gwamnatin Amurka ta dakatar da sayarwa Saudiya makamai domin kisan kiyashin da take yiwa Al'ummar kasar Yemen
Mista Rand Paul Sanatan jam'iyar Repablicain na jihar Kentucky ya bayyana cewa Kasar Saudiya ita ce sanadiyar muwuyacin halin da Al'ummar kasar Yemen ke ciki, bayan kallafafen yakin da ta kaddamar a kansu domin haka ya zamanto wajibi magabatan kasar Amurka su dakatar da sayawar magabatan Saudiyan makamai.
Mista Rand Paul ya kara da cewa Kasar Saudiya ita ce ke goyon bayan duk wasu kungiyoyi masu tsatsaurin ra'ayi na Duniya tare kuma da taimaka musu da kudade sannan kuma so da dama an samu kasar da laifin take hakin bil-adama.
Wannan firici na Mista Paul na zuwa ne a yayin da Gwamnatin Amurka ta gabatar da kudirin sayawar wa kasar Saudiya makamai da kayan yaki na zamani har na dalar Amurka bilyan 110 a gaban Majalisar, kudirin da bai samu amincewa ba, inda sanatoci 53 suka kada kuri'ar rashin amincewa a gaban sanatoci 47 da suka amince.
A yayin ziyarar da Shugaba Trump na Amurka ya kai birnin Riyad ya kula yarjejjeniyar sayarwa magabatan Saudiyar makamai na bilyan 110 na $.