Wutar Daji Ta Hallaka Mutane 19 A Kasar Portugal
https://parstoday.ir/ha/news/world-i21402-wutar_daji_ta_hallaka_mutane_19_a_kasar_portugal
Wutar Daji a yankin Leiria dake tsakiyar kasar Portugal yayi sanadiyar mutuwar mutane 19 tare da jikkata wasu 20 na daban
(last modified 2018-08-22T07:00:15+00:00 )
Jun 18, 2017 01:15 UTC
  • Wutar Daji Ta Hallaka Mutane 19 A Kasar Portugal

Wutar Daji a yankin Leiria dake tsakiyar kasar Portugal yayi sanadiyar mutuwar mutane 19 tare da jikkata wasu 20 na daban

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto Jorge Gomez Minista mai bayar da shawara a Ma'aikin cikin gidan Portugal a daren jiya Assabar na cewa daga cikin mutane 19 da suka rasa rayukan su 3 sun rasu ne sanadiyar shagar hayakin gobarar, 16 kuma sun rasu ne a yayin da motar ke ficewa cikin dajin daidai lokacin da wutar ta tashi.

Karuwar yanayin zafi , ko wata shekara na yi sandiyar tashin wutar Daji a kasar ta Portugal, a shekarar da ta gabata, wutar Dajin a arewa maso yammacin kasar yayi sanadiyar rusa gidaje da dama tare da toshe hanyoyin isa zuwa ga yankin da wutar da tashi.