Mutane 62 Suka Mutu A Gobara Daji a Portugal
https://parstoday.ir/ha/news/world-i21418-mutane_62_suka_mutu_a_gobara_daji_a_portugal
Hukumomi a Portugal sun ce a kalla mutane 62 ne suka mutu a mummun gobara gandun daji data aukawa yankin Leiria a tsakiyar kasar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 18, 2017 09:59 UTC
  • Mutane 62 Suka Mutu A  Gobara Daji a Portugal

Hukumomi a Portugal sun ce a kalla mutane 62 ne suka mutu a mummun gobara gandun daji data aukawa yankin Leiria a tsakiyar kasar.

Gobara wacce ta tashi  jiya da rana a garin Pedrogao Grande, ta kuma yi sanadin jikkatar mutane sama da hamsin ciki har da jami'an kwana-kwana guda takwas a cewar  sakataren gwamnatin na harkokin cikin gidan kasar Jorge Gomes.

Wannan dai ita ce gobara daji mafi muni da aka taba gani a shekarun baya bayan nan a wannan kasa a cewar fira ministan kasar Antonio Costa.

An dai zuba jami'an kashe gobara kimanin 900 da kuma motoci 300 domin kashe wutar wacce har tsakiyar wannan ranar tana ci a wasu bangare.

Tuni dai gwamnatin kasar ta ayyana zamen makoki na kwanaki uku tun daga yau Lahadi domin juyayin wandanda suka mutu a wanna iftila'in.