Rasha Ta Gargadi Amurka A Kan Take-Takenta A Syria
https://parstoday.ir/ha/news/world-i21684-rasha_ta_gargadi_amurka_a_kan_take_takenta_a_syria
Gwamnatin kasar Rasha ta bukaci Amurka da ta daina kai hare-hare a kan sojojin Syria da kuma jiragen yakin kasar.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jun 27, 2017 00:48 UTC
  • Rasha Ta Gargadi Amurka A Kan Take-Takenta A Syria

Gwamnatin kasar Rasha ta bukaci Amurka da ta daina kai hare-hare a kan sojojin Syria da kuma jiragen yakin kasar.

Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha Sergey Lavrov ne ya bayyana hakan a zantawa da ta hanada jiya ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, inda ya bayyana masa cewa Rasha ba za ta amince da abin da Amurka ke yi na kai hare-hare a kan sojojin Syria ba.

Lavrov ya ce babu wani dalilin da Amurka za ta fake da shi wajen harbo jiragen yakin Syria da ke kai hare-hare a kan sansanonin ISIS, a lokaci guda kuma ta ce tana yaki ne da ISIS a Syria.

Ko a jiya Amurka ta sake maimaita zarginta a kan sojojin Syria ta gano suna da shirin yin amfani da makamai masu guba, lamarin da Rasha ke kallonsa a matsayin wani sabon shirin da Amurka take shiryawa domin bullo da wata fitinar ta daban a kan gwamnatin Syria.

A lokutan baya ma gwamnatin Amurka ta zargi gwamnatin Syria da yin amfani da makamai masu guba a ynakin Khanshekhun da ke gundumar Idlib, inda ta fake da hakan domin kai hari a wani filin jiragen sojin Syria, duk kuwa da cewa har yanzu Amurka ta kasa kawo dalili da ke tabbatar da zargin nata  akan gwamnatin Syria.

Wasu na ganin cewa daga cikin biliyoyin dalolin da Trump ya karba a taron Riyadh har da na kirkiro wata hujja domin daukar matakan soji da za su kai ga kifar da gwamnatin Syria, wadda Amurka da 'yan korenta suke yaki da ita tsawons hekaru 6 ta hanyar yin amfani da 'yan ta'addan wahabiyyah takfiriyya na ISIS, kuma har yanzu ba su iya cin galaba a kanta ba.