Paparoma Francis Ya Gargadi Shuwagabannin G20 Kan Yake Yake A Duniya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i21996-paparoma_francis_ya_gargadi_shuwagabannin_g20_kan_yake_yake_a_duniya
Shugaban cocin Catholica Na Paparoma Francis ya bukaci kasashen duniya da su kawo karshen yake-yaken da basu da amfani da kuma gasar kera makamai a duniay.
(last modified 2018-08-22T07:00:21+00:00 )
Jul 07, 2017 14:32 UTC
  • Paparoma Francis Ya Gargadi Shuwagabannin G20 Kan Yake Yake A Duniya

Shugaban cocin Catholica Na Paparoma Francis ya bukaci kasashen duniya da su kawo karshen yake-yaken da basu da amfani da kuma gasar kera makamai a duniay.

Kamfanin dillancin Labaran IRNA ya nakalto Paparoman yana fadar haka a yau jumma'a a lokacinda yakewa shuwagabannin kungiyar G20 a birnin Hambur na kasar Jamus.

Shugaban mazhbar Catholica ya bukaci shuwagabannin kasashen G20 da su fifita tattaunawa da kuma hanyoyin diblomasiyya wajen warware matsalolin tsakanin kasashen duniya su kuma bada himma wajen tallafawa marsa galihu a cikin al-ummun duniya. 

Kungiyar G20 sun hada da kasashe 19, wato Agentina, Australia, brazil, Sin, Jamus, Faransa, Britania, India, Indonasia, Italia, Canada, Japan, Korea ta Kudu, Mexoco, Rasha, Saudia, Afrika ta Kudu, Turkia, Amurka da kuma Tarayyar Turai. 

A yau Jumma'a ce shuwagabannin Kungiyar suka fara taron kwanaki biyu a birnin Hamburg na kasar Jamus.