Shugabannin Kungiyar G20 Sun Lashi Takobin Yakar Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/world-i22024-shugabannin_kungiyar_g20_sun_lashi_takobin_yakar_ta'addanci
Shugabannin kungiyar G20 ta kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya sun lashi takobin inganta hadin kai don yaki da ayyukan ta'addanci da masu samar musu da kudi.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jul 08, 2017 13:28 UTC
  • Shugabannin Kungiyar G20 Sun Lashi Takobin Yakar Ta'addanci

Shugabannin kungiyar G20 ta kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya sun lashi takobin inganta hadin kai don yaki da ayyukan ta'addanci da masu samar musu da kudi.

Wata sanarwar da aka fitar a a ranar farko ta taron dake gudana a binnin Hamburg na Jamus, ta ce shugabannin kasashen da ke  samar da kashi 85 cikin dari na kayyayaki a duniya, sun jadadda cewa, akwai bukatar aiwatar da dukkan matakan yaki da ta'addanci bisa biyayya da ka'idojin MDD da dukkan dokokin kasa da kasa.

Shugabannin sun amince su gaggauta musayar bayanai tare da amfani da duk hanyoyin dake akwai na musayar bayanai, musammam ma hanyoyi musayar bayanai na rundunar 'yan sanda ta kasa da kasa wato INTERPOL.

Game da hanyoyin da 'yan ta'adda ke samun kudi kuwa, shugabannin sun tabbatar da kudurinsu na katse dukkan hanyoyi da dabarun samar da kudaden, suna masu kira da a gaggauta aiwatar da kudurin kwamitin sulhu na MDD na datse dukkan hanyoyin samun kudi ga 'yan ta'adda.