Mutane 16 Suka Mutu Bayan Faduwar Jirgin Yakin Amurka A Misisippi
Mutane 16 aka tabbatar da mutuwarsu ya zuwa yanzu bayan faduwar jirgin saman daukar kayan yaki mallakin kasar Amurka
Tashar television ta Presstv ta bayyana cewa jirgin ya fadi ne a jiya litinin da yamma kuma yana dauke da sojojin 16, kuma tuni an gano gawakin mutane 15 daga cikinsu.
Majiyar Ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa jirgin kirar USMC KC-130 ya fada a ranar 10 ga watan Yuli a yankin Misisippi, amma kama har yanzun ba'a gano illar faduwarsa ba. Ma'aikatar da kara da cewa ana amfani da jirgin wajin jigilar kayaki sannan a wasu lokuta a matsayin mai dakon makamacin jiragen saman yaki.
Labarin bai bayyana cewa ko akwai farar hula cikin jirgin ba. Majiyar ta kara da cewa jirnin yana da garkuwan makaman kakkabo jiagen sama masu karfi.