Za A Fitar Da Jami'an Diflomasiyar Amurka 30 Daga Kasar Rasha
Rasha ta ce Za ta fitar da jami'an Diflomasiyar Amurka 30 daga cikin kasar a matsayin mayar da martani na fitar da jami'an Dipulomasiyar kasar 35 daga Amurka a watan Decembar shekarar da ta gabata.
Kafar watsa labaran yanar gizo na Rasha Isocita ya nakalto wani jami'in Ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar na cewa ganin cewa gwamnatin Amurka bata bukatar magance rikicin Diflomasiyar dake tsakanin kasashen biyu, don hakan kasar za ta kori jami'an Dipulomasiyar Amurka 30 daga cikin kasar a matsayin mayar da martani na fitar da jami'an Dipulomasiyar kasar 35 daga Amurka a watan Decembar shekarar da ta gabata.
Wannan mataki na zuwa kwanaki uku bayan ganawar farko na Shugaban kasar Amurka Donal Trump da takwaransa na Rasha Viladimin Putin a birnin Hamburg na kasar Jamus, inda aka yi tunanin cewa Shugabanin biyu za su gyara dangantarar dake tsakanin kasashen biyu.
A watan Decembar 2016 da ta gabata ce, tsohon shugaban kasar Amurka Barak Obama ya kori jami'an Dipulomasiyar Rasha 35 daga cikin kasar bisa zarkin su da yin katsa landan a zaben Shugabancin kasar.