Venezuella : 'Yan Adawa Zasu Fito Zanga-zanga Duk Da Haramcin Gwamnati
https://parstoday.ir/ha/news/world-i22650-venezuella_'yan_adawa_zasu_fito_zanga_zanga_duk_da_haramcin_gwamnati
'Yan adawa a Venezuela sun ce zasu fito zanga-zanga gama gari a ranakun Juma'a zuwa Lahadi ranar da za'a gudanar da zaben wakilan majalisar dokokin kasar da shugaban Nicolas Maduro ya bukata.
(last modified 2018-08-22T07:00:27+00:00 )
Jul 27, 2017 23:32 UTC
  • Venezuella : 'Yan Adawa Zasu Fito Zanga-zanga Duk Da Haramcin Gwamnati

'Yan adawa a Venezuela sun ce zasu fito zanga-zanga gama gari a ranakun Juma'a zuwa Lahadi ranar da za'a gudanar da zaben wakilan majalisar dokokin kasar da shugaban Nicolas Maduro ya bukata.

Wannan dai na zuwa ne duk da haramcin gwamnatin na gudanar da zanga-zanga.

Mukadancin shugaban majalisar da 'yan adawa ke jagoranci, Freddy Guevara, ya yi kira ga duk 'yan kasar dasu fito zanga-zanga daga yau Juma'a har zuwa Lahadi domin kalubalantar matakin gwamnatin Maduro.

A ranar Alhamis wata sanarwa da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar ta haramta duk wata zanga-zanga da taruka da gangami, saboda kaucewa cikas din da hakan zai iya haifarwa ga gudnar da zaben.

Kawo yanzu dai mutane 108 ne suka rasa rayukansu a ci gaba da zanga-zanga kyammar gwamnatin shugaba Nicolas Maduro a wannan kasa ta Venezuela.