Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Kawo Karshen Killace Yankin Zirin Gaza
https://parstoday.ir/ha/news/world-i23124-majalisar_dinkin_duniya_ta_jaddada_kawo_karshen_killace_yankin_zirin_gaza
Kakakin Kwamitin Kolin Kare Hakikin Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kawo karshen killace yankin Zirin Gaza na Palasdinu.
(last modified 2018-08-22T11:30:32+00:00 )
Aug 12, 2017 11:52 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Kawo Karshen Killace Yankin Zirin Gaza

Kakakin Kwamitin Kolin Kare Hakikin Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kawo karshen killace yankin Zirin Gaza na Palasdinu.

Kakakin Kwamitin Kolin Kare Hakkin Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya Ravina Shamdasani ta bayyana tsananin damuwarta kan mummunan halin da al'ummar yankin Zirin Gaza suke ciki; Tana mai bayyana cewa: A karkashin dokokin kasa da kasa hakkin kare al'ummar Palasdinu yana kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ne da ta mamaye yankunan Palasdinawan.

Har ila yau kakakin Kwamitin Kolin Kare Hakkin na Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan irin mummunan sakamakon da rashin wutan lantarki a yankin Zirin na Gaza zai haifar a harkar kiwon lafiya da rashin samun tsabtaceccen ruwan sha.