Spain: Kungiyar Da'esh Ta Dauki Alhakin Kai Harin Barcelona
Aug 18, 2017 02:09 UTC
A jiya alhamis ne dai aka kai mummunan harin ta'addanci a birnin Barcelona na kasar Spain wanda ya ci rayukan mutane da dama da kuma jikkata wasu.
An kai harin ne dai ta hanyar amfani da motar da ta bi ta kan mutane a yankin Las Ramblas da ke tsakiyar birnin na Barcelona.
Jami'an gwamnatin yankin na Catalonia sun tabbatar da mutuwar mutane 12 da kuma jikkatar wasu fiye da 80.
Yan sanda sun ce wanda ya kai harin sunan shi Driss Oukabir, kuma tuni sun kashe shi.
Kungiyar Da'esh dai ta sha kai hare-hare irin wadannan a cikin kasashen turai daban-daban da suka hada da Birtaniya.