Zanga-zangar Kyammar Wariyar Launin Fata A Amurka
Aug 20, 2017 06:45 UTC
Rahotanni daga Amurka na cewa dubbun dubatar mutane ne suka halarci wata gagarimar zangar-zangar kyammar launin fata a birnin Boston.
Ko baya ga kyammar launin fata masu zanga-zanga da yawan su ya kai kimanin 40,000 na tir da kalamen baya bayan nan na shugaban kasar Donald Trump bayan rikicin da ya faru a birnin Charlottesville.
Bayanai daga yankin sun ce an fuskanci dan artabu tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar, an kuam samu wasu da suka jikkata baya ga wasu 27 da 'yan sanda suka cafke.
Tags