WFP: Musulman Rohingya Na Bukatar Taimakon Abinci Na Gaggawa
(last modified Fri, 15 Sep 2017 05:49:30 GMT )
Sep 15, 2017 05:49 UTC
  • WFP: Musulman Rohingya Na Bukatar Taimakon Abinci Na Gaggawa

Cikin wani rahoto da ta fitar, Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) ta bayyana cewar sama da musulmin Rohingya na kasar Myammar dubu dari da suka gudu daga kasar zuwa Bangladesh don tsira da rayukansu suna cikin matsanancin halin rashin abinci da suke bukatar taimakon gaggawa.

Yayin da take magana kan wannan lamarin, kakakin Hukumar Abinci ta Duniya Frances Kennedy ta ce da dama daga cikin musulmin Rohingya da suke gudun hijira a kasar Bangladesh din sun dauki kwanaki ba su ci abinci ba, suna ma bukatar samun wani waje ne da za su zauna tukun.

Jami'ar Hukumar Abinci ta Duniya ta ci gaba da cewa irin yanayin da musulmin suke ciki lamari ne mai tada hankali da ke bukatar agaji na gaggawa.

A bisa kididdigar Majalisar Dindikin Duniyan dai sama da musulmin Rohingya dubu 300 ne suka gudu daga kasar da damansu suna cikin kasar Bangladesh don tsirar da kansu daga kisan kiyashin da sojoji da mabiya addinin Buddha na kasar Myammar din suke musu.