MDD Na Bukatar Dala Miliyan 200, Don Agazawa 'Yan Rohingyas
Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tana bukatar kudade da yawansu ya kai Dala Miliyan 200 a cikin watanni shida masu zuwa domin taimakawa 'yan gudun hijira Rohingya dake gujewa kisan kare dangin da ake musu a Myammar.
Kawo yanzu dai alkalumman da MDD ta fitar sun nuna cewa adadin musulmun 'yan Rohingyas da sukayi hudun hijira a kasar Bangaladash ya kai 420,000.
A farkon watan nan ne na Satumba MDD ta mika kiran gaggawa ga kasashen duniya na neman Dala Miliyan 78 don agazawa mutanen, saidai a cewar jagoran kula da ayyukan jin kai na MDD a Bangaladash Robert Watkins, ana bukatar kudaden da suka zarta hakan don shawo kan matsalar.
Kafin hakan dai kungiyar likitoci marar iyaka ta MSF, ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun bala'i na barkewar wasu cututuka irinsu kwalera ko amai da gudawa da cutar kyanda a kudancin kasar ta Bangaladesh a cikin irin wannan yanayi na kwararar 'yan gudun hihija na Rohingyas.
A halinda a ake ciki dai kasar Saudiyya ita ma ta sanar da aikewa da wani tallafi da ya kunshi ton 100 na abunci da runfuna da katifofi, a yayin da ita kuma Amurka ta alkawarta bada tallafi na kudade dala miliyan 32 ga kasar Bangaladash don taimaka mata wajen shawo kan matsalar.