MDD:Musulmin Rohingya Sun Fuskanci Wahalhalu Masu Yawa
(last modified Mon, 25 Sep 2017 05:42:31 GMT )
Sep 25, 2017 05:42 UTC
  • MDD:Musulmin Rohingya Sun Fuskanci Wahalhalu Masu Yawa

Babban kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na MDD Filippo Grandi ya bayyana cewa musulmi 'yan kabilar Rohingya sun fuskanci wahalhalu masu yawa domin haka suna bukatar agajin gagguawa mai yawa.

Hukumar gidan telbijin da radio na kasar Iran ya nakalto Filippo Grandi a jiya lahadi na cewa mahimin taimakon da musulmi 'yan kabilar Rohingya suke bukata a halin yanzu samar musu da mazugunin da ya dace da su.

Babban kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na MDD ya kara da cewa wasu daga cikin musulmin Rohingya sun samu lahani tun kafin suyi hijira, wasunsu kuma ma sun fuskanci matsala a cikin kwakwalansu, wanda kuma magance wannan matsala yana bukatar shekaru masu yawa.

A yayin da yake ishara kan zalincin da gwamnatin Myammar ta yiwa musulimi 'yan kabilar Rohingya a kasar ya ce shakka babu wadannan mutane sun dace su samu kulawa ta musaman da kuma goyon bayan kungiyoyin kasa da kasa na duniya.

Tun daga ranar 25 ga watan Augustan da ta gabata ne , sojojin gwamnatin myammar da mabiya addinin Buddha masu tsaurin ra'ayi suka afka wa musulmin Rohingya a jihar Rakhine na kasar da kisa inda ya zuwa yanzu suka kashe daruruwa da kuma tilasta wa wasu dubbai zama 'yan gudun hijira.