Sharhi: Kuri'ar Raba Gardamar Yankin Kurdawan Kasar Iraki
https://parstoday.ir/ha/news/world-i24349-sharhi_kuri'ar_raba_gardamar_yankin_kurdawan_kasar_iraki
A yau Litinin ne ake sa ran za a gudanar da zaben raba gardama dangane da makomar yankin Kurdestan na kasar Iraki, a kokarin da 'yan siyasar yankin suke yi na balle yankin daga kasar Iraki da kafa kasar Kurdawa mai cin gashin kanta.
(last modified 2018-08-22T07:00:44+00:00 )
Sep 25, 2017 02:29 UTC
  • Sharhi: Kuri'ar Raba Gardamar Yankin Kurdawan Kasar Iraki

A yau Litinin ne ake sa ran za a gudanar da zaben raba gardama dangane da makomar yankin Kurdestan na kasar Iraki, a kokarin da 'yan siyasar yankin suke yi na balle yankin daga kasar Iraki da kafa kasar Kurdawa mai cin gashin kanta.

A ranar 7 ga watan Yunin wannan shekarar ta 2017, shugaban yankin Kurdestan din na kasar Iraki Mas'ud Barazani ya sanar da aniyar hukumar tasa ta gudanar da kuri'ar raba gardamar da nufin raba yankin da kasar Iraki. To sai dai kuma tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu musamman cikin 'yan kwanakin nan an ta samun labarai da rahotanni masu karo da juna dangane da yiyuwar jinkirta gudanar da zaben, to amma ko a jiya Lahadi, Mas'ud Barzanin ya sake jaddada aniyarsa ta gudanar da zaben yana mai cewa babu gudu babu ja da baya.

Tsawon makonnin da suka gabata dai kasashen duniya da cibiyoyi na kasa da kasa da dama sun bayyana rashin amincewarsu da wannan zaben wanda firayi ministan kasar Irakin Haidar al-Abadi ya kira shi da "Wasa da garwashin wuta", to amma duk da hakan dai Mas'ud Barzani ya tsaya kyam da cewa lalle zai gudanar da zaben raba gardamar lamarin da ya sanya da dama tambayar cewa wai mene ne dalili da manufarta ta gudanar da wannan zaben? Me ya ke son cimma ne?

To masana al'amurran yau da kullum dai suna ganin akwai wasu manufofi guda uku da Barzanin yake son cimmawa: 

Manufar farko ita ce kokarinsa na bayyanar da kansa a matsayin wani shugaba kana jagoran Kurdawan da kuma halalta ci gaba da rike shugabancin yankin Kurdawan da yayi duk kuwa da rashin halalcin hakan.

Manufa ta biyu da Barzani yake son cimmawa ta hanyar gudanar da kuri'ar raba gardamar ballewa daga kasar Irakin ita ce kokarin mai da batun ballewa daga Iraki ya zamanto wata bukata ta Kurdawan da zai dinga amfani da ita wajen cimma wasu manufofi na siyasa da yake da su. Wanda hakan yana daga cikin dalilan da ya sanya da dama daga cikin kasashen duniya kin amincewa da kuri'ar raba gardamar saboda da dama daga cikin kasashen duniya suna da irin wadannan kabilu 'yan tsiraru wadanda idan kowa ya ce zai yi kokarin ballewa da kafa kasarsa ta daban bisa tushe na kabila to babu abin da zai rage na hadin kan kasashe in ba dan kadan ba.

Manufa ta uku kuma ita ce sanya kasar Irakin da ma yankin baki daya cikin wani yanayi na rikici da rashin tabbas. Don kuwa tun ba da jimawa ba da dama daga cikin kasashen duniya da ma wadanda suke makwabtaka da Irakin sun bayyana wannan kokari na Barzanin a matsayin wasa da garwashin wuta. A saboda haka idan har wadannan kasashe musamman Iran, Turkiyya da Siriya suka aiwatar da barazanar da suka yi akwai yiyuwar zubar da jini, idan kuma ba su yi hakan ba, to suka dauki mataki na ruwan sanyi, to kuwa Kurdawan za su fuskanci matsaloli na tattalin arziki da zamantakewa.

Ala kulli hal, kowane guda daga cikin wadannan abubuwa guda, wato amfani da karfin soji ko kuma amfani da makami na tattalin arziki da zamantakewa, babban wanda zai cutu daga hakan su ne dai talakawan Kurdawan kafin ya je ga su masu kokarin gudanar da kuri'ar raba gardama da iyalansu wadanda da dama daga cikinsu an ce iyalan na su ma ba sa nan a yankin na Kurdestan.