Unicef Na Bukatar Dala Milyan 76 Don Taimakawa Yaran Rohingya
Asusun kula da yara kankana na Majalisar Dinkin Duniya cewa da Unicef, ya ce yana bukatar dalar Amurka Milyan 76 domin agazawa yara 'yan kabilar musulmin Rohingya.
Asusun na Unicef ya bukaci ga kasashen duniya dasu taimaka don samun wannan kudaden domin tallafawa yaran 'yan gudun hijira Rohingya dake bukatar tallafin gaggawa a Bangaladash.
Kawo yanzu sama da rabin milyan na musulmin Rohingya ne suka tsallaka iyaka zuwa Bangaladash don gujewa kisan kiyashin da jami'an tsaro da 'yan addinin Buda na Myammar ke musu.
Alkalumman da MDD ta fitar sun nuna cewa kashi 60% na 'yan gudun hijira Rohingya din yara ne, kuma yawan yaran dake cikin bukata ya kai dubu dari bakwai da ashirin (720,000) a cewar asusun na Unicef.
Akasarin yaran a cewar MDD na fama da matsalar karamcin abinci mai gina jiki wato tamowa sannan kuma rayuwarsu tana cikin hadari kasancewar yanayin da suke ciki a sansanonin da ake kebe musu a kasar ta Bangaladah.