Amurka: Trump Ya Janye Goyan Bayan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da janye goyan bayan kasarsa ga yarjejeniyar nukiliyar da mayan kasashen duniya suka cimma da Iran.
Wanann dai ya nuna shugaba Donald Trump na Amurka ya yi amai ya lashe dangane da batun yarjejeniyar nukiliyar Iran wacce ya yi alkawalin ganin bayan ta.
A jawabinsa na yau Juma'a da aka dade ana jira, Trump ya ce baya goyan bayan yarjejeniyar wacce akayi tsammanin zai sanar da janyewar kasarsa daga cikinta, duk da cewa ya ce zai iya kawo karshenta a koda yaushe.
Trump dai ya ce Iran bata muntunta yarjejeniyar da aka cimma da ita ba a 2015, don haka zai mika batun ga gwamnatinsa da majalisar kasar don ta dau mataki akan Iran ciki har da yiwuwar kakaba mata takunkumi a wasu bangarori.
A matsayin maida martani kan jawabin na Trump, shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya ce wannan ya fiddo fili kiyaya da Amurka kewa Iran.