EU Ta Yi Alkwarin Karba Bakin Haure 34.000
https://parstoday.ir/ha/news/world-i25482-eu_ta_yi_alkwarin_karba_bakin_haure_34.000
Kungiyar tarayya Turai ta EU, ta alkawarta samar da matsugunnai kimanin 34,000 ga 'yna gudun hijira da suka fito kai tsaye daga Afrika da kuma gabas ta Tsakiya.
(last modified 2018-08-22T07:00:59+00:00 )
Nov 15, 2017 13:46 UTC
  • EU Ta Yi Alkwarin Karba Bakin Haure 34.000

Kungiyar tarayya Turai ta EU, ta alkawarta samar da matsugunnai kimanin 34,000 ga 'yna gudun hijira da suka fito kai tsaye daga Afrika da kuma gabas ta Tsakiya.

Wannan dai na zuwa bayan sukar da hukumar kare hakkin bil adama na MDD ya yi wa kungiyar akan siyasar kungiyar hadin gwiwa ta tsakanin kungiyar ta EU kasar Libiya.

A watan Satumban da ya gabata, kwamitin zartarwa na kungiyar ta EU ya bayyana anniyarsa ta karbar bakin haure 50,000 wadanda suka fito da Libiya ko kuma Nijar a cikin shekaru biyu a matsayin wata hanya ta samun mafita ga kwararar bakin hauren dake rasa rayukansu a kokarin tsallakawa ta taku zuwa turai. 

Kafin hakan dai shugaban kungiyar kare hakkin bil adama ta MDD, Zeid Ra'ad Al Hussein, ya cacaki siyasar kungiyar ta tarayya turai da Libiya kan halin da ake tsare bakin haure a kasar Libiya, wanda ya danganta da rashin imani siyasar ta kungiyar EU ta taimakawa jamia'n tsaron gabar ruwan Libiya na cafkewa da kuma mayar da bakin hauren.