Shahadar Imam Ridha (AS)
Nov 19, 2017 03:01 UTC
A yau lahadi 30 ga watan Safar ne mabiya ahul Bait (a.s) Suke juyayin shahadar Imam Ridha, (a.s)
Imam Ridha wanda shi ne Imami na takwas a jerin Imaman ahlul baiti (a.s) ya yi shahada ne a ranar karshe ta watan Safar na shekarar hijira kamariyyah ta 203 a zamanin halifancin Ma'amun na daular Abbasiyya.
Anan jamhuriyar musulunci ta Iran ana raya dare da ranar shahadar Imam Ridha (a.s) da juyayi tare kuma da yin bayani akan rayuwarsa a cikin masallatai da kuma Husainiyoyi. Bugu da kari, rana ce ta hudu.
Sashen Hausa na muryar jamhuriyar musulunci ta Iran na isar da ta'aziyyarsa ga dukkanin masoya iyalan gidan manzon Allah (s.a.wa.)