Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Ratko Mladich
https://parstoday.ir/ha/news/world-i25657-hukuncin_daurin_rai_da_rai_kan_ratko_mladich
Daga karshe dai bayan shekaru 4 da fara shari'a, kotun hukunta masu laifuffukan yaki a birnin Hague ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai kan Ratko Mladich wanda ya fi shahara da mahaucin Bosnia a jiya Laraba.
(last modified 2018-08-22T07:01:02+00:00 )
Nov 23, 2017 02:55 UTC
  • Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Ratko Mladich

Daga karshe dai bayan shekaru 4 da fara shari'a, kotun hukunta masu laifuffukan yaki a birnin Hague ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai kan Ratko Mladich wanda ya fi shahara da mahaucin Bosnia a jiya Laraba.

An sanya Ratko Mladich a cikin jerin wadanda ake tuhuma da laifuffukan yaki tun ana cikin yakin Bosnia Hadzogovina, sannan bayan an kawo karshen yakin a shekara ta 1995, Mladich ya boye, na tsawon shekaru 16 a wani gida a birnin Belgrate, wato har zuwa shekara ta 2011 aka gano shi. 

Kotun ta birnin Hague ta yanke hukunci kan Mladich, dan shekara 74 a duniya ne a jiya Laraba  bayan yakin Bosnia da shekaru 22, sannan ta same shi  laifuffuka 10 cikin 11 da aka tuhume shi da su, daga cikinsu akwai kisan Musulman Bosnia 8,000 a garin Srebrenica da ya jagoranta a lokacin yakin.

Don yawan mutanen da aka kashe a wannan garin, har yanzu, a duk ranar tunawa da kisan ta zagayo a ko wace shekara, ana bisne wadanda aka gano gawakinsu a kaburburan gama gari a cikin shekara. 

Sai dai abin da har yanzun kotun birnin Haque bata tabo batun sa ba, dangane da abin da ya faro a yakin Bosnia a tsakanin shekara 1992- 1995 shi ne rawar da sojojin MMD yan kasar Holand, wanda aka dorawan nauyin kare Musulman Bosnia a garin Srebrenica, bayan da aka bayyana garin a matsayin tudun na tsari ga musulman Bosnia, amma kuma a gabansu sojojin sabia karkashin jagorancin wannan mahaucin -Ratko Mladich- suka shiga garin  suka aiwatar da wannan kisan kiyashin ba tare da sun tanka masu ba. 

Ko wa ya cewa,  bayan wargajewar tarayyar Yugoslavia, yankunan kasar daban daban sun ware daga tarayyar, ba tare da wata matsala ba. Slovenia ta yi rigima da sabiyawa na kwanki 10 kacal, ta sami 'yencin kanta, a yayinda Koroshia ta shiga yaki da sabiyawa na tsawon watanni 3 kacal aka amince da bellewarta. Sai kuma kasar Magdonia ta balle daga tarayyar Yugoslavia ba tare da zubar da jinin ba. Hakama kasar Montnigro bata sami wata matsala da sabiyawa ba,  ta balle daga tarayyar ta Yugoslavia. Amma bellewar Bosnia Herzegovina ya zama, sai da aka zubar da jinin mutanen da ba'a taba zubar da jina mai yawa irinsa ba  a turai tun bayan yakin duniya na biyu. Wannan bai faru ba sai don su musulmi ne.

A lokacin an ruwaito Priministan kasar Britania na lokacin , John Major,  yana cewa  ba zasu taba yarda a kafa wata kasar Musulmi a Turai ba. Wannan ya nuna cewa shuwagabannin kasashen Turai da dama sun karfafawa Sabiyawa guiwa a laifuffukan da suka aikata a kasar Bosnia. 

Akalla musulman Bosnia dubu 100 aka kashe a wannan yakin, mutum dubu 8000 daga cikinsu, Ratko Mladich ya jagoranci kisansu  a garin  Srebrenica kadai.