An Cimma Yarjejeniyar Mayar Da 'Yan Rohingya Gida
(last modified Thu, 23 Nov 2017 15:14:57 GMT )
Nov 23, 2017 15:14 UTC
  • An Cimma Yarjejeniyar Mayar Da 'Yan Rohingya Gida

Kasashen Myanmar da Bangaladash sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar ta mayar da 'yan gudun hijirar musulmin Rohingya gida.

Wat sanarwa da ma'aikatar harkokin waje Bangaladash ta fitar ta ce za'a mayar da 'yan Rohingya gida a cikin watanni biyu masu zuwa, saidai ba tare da bayyana adadinsu ba ko kuma sharidodin mayar dasu giba.

Tuni dai wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama suka nuna damuwarsu akan wannan yarjejeniyar, kasancewar babu tabas akan halijn da ake ciki a yankin na Rakhine.

Kimanin 'yan gudun hijira Rohingya su 620,000 suka tsallaka kasar Bangaladash domin kauracewa kisan kiyashin da jami'an tsaro Myanmar ke masu.

MDD dai ta danganta abunda ke faruwa a yankin na Rakhine dake yammacin kasar ta Myanmar a matsayin yunkurin share wata kabila daga doron kasa.