Venezuela : Tattaunawa Tsakanin Gwamnati Da 'Yan Adawa Ta Yi Armashi
Wakilan gwamnati da na 'yan adawa a Venezuela sun kamalla zagayen farko na tattaunawar da suke a Jamhuriyar Dominican domin samun mafita a rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar.
Duk da cewa bangarorin basu cimma matsaya ba, amma an samu ci gaba sosai a tattaunawar a cewar shugaba Danilo Medina na Jamhuriyar ta Dominican.
Kasancewar bangarorin basu kai ga cimma matsaya ba zasu sake haduwa a birnin Saint-Domingue a ranar 15 ga watan nan na Disamba da muke ciki, da zumar samun mafita a cewar sanarwar bai daya ta karshen tattaunawar.
Sanarwa kashen tattaunawar ta ce dukkan bangarorin biyu sun nuna da gaske su ke a yunkurin samun fahimtar juna kan mummunan rikicin siyasa dana tattalin arziki da ya ki ci yaki cinyewa a kasar ta Venezuela.