Koriya Ta Arewa Ta Sake Harba Makamai Masu Linzami
https://parstoday.ir/ha/news/world-i2614-koriya_ta_arewa_ta_sake_harba_makamai_masu_linzami
Kasar Koriya ta arewa ta sake harba makamai masu linzami biyu a safiyar wannan Juma'a kamar yadda hukumomin Amurka da Koriya ta kudu suka tabbatar.
(last modified 2018-08-22T06:58:00+00:00 )
Mar 18, 2016 06:52 UTC
  • Koriya Ta Arewa Ta Sake Harba Makamai Masu Linzami

Kasar Koriya ta arewa ta sake harba makamai masu linzami biyu a safiyar wannan Juma'a kamar yadda hukumomin Amurka da Koriya ta kudu suka tabbatar.

bayanai daga yankin sun ce an harba makamin farko ne da misalin karfe shida saura agogon wurin, inda daya daga cikin makamin ya ci nisan kilomita 800 a sararin samaniya kafin daga bisani ya tarwatse cikin teku, na biyun kuma na harba shi bayan mintina 20 da harbin farko, kuma dukkanin makaman kirar Rodong ne mai matsakaicin zango da kuma ke iya zuwa kasar Japan.

wannan dai na zuwa kwanan guda bayan da shugaban Amurka Barack Obama ya rattaba hannu kan kudirin kakaba sabin takunkumai ga koriya ta Arewar saboda harba ire-iren wadanan makaman da aka haramta mata.