EU Ta Jadada Matsayinta Kan Qudus
kungiyar tarayya Turai ta EU ta jadada matsayinta akan birnin Qudus, bayan matakin shugaba Trump na ayyanasa a mastayin babban birnin yahudawan mamaya na Isra'ila.
A yayin da take ganawa da Firaminitan Isra'ilar da ya kai ziyara a birnin Brussels a yau, shugabar kula da harkokin waje ta kasashen turan, Federica Mogherini, ta ce matsayin kungiyar tarayyar EU kan Qudus yana nan daram.
Kana kuma a cewarta, hanya daya tilo ta gakia ita ce Qudus ya kasance babban birnin Palastinu da Israilar kasashe biyu makoftan juna da zau zauna cikin zaman lafiya biza yarjejeniyar da kasashen duniya suka shafa iyakokin a 1967.
Saidai da yaka bayyani Netanyahu ya ce matakin Trump kan Qudus wata hanya ce ta samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, yana mai fatan nan gabas kasashen turan su ma zasu bi sahun Amurka.
Saidai a cewar Madam Mogereni wannan tunaninsa, amma a yanzu kasashe 28 na kan matsayinsu na yin tir da matakin na Trum.
Ko a yayin ziyara da ya kai a birnin Paris, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci Netanyahu din da ya daina gine-gine a yankunan Falastinawa da kuma kaddamar da tattaunawa domin kawo zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.