Tsohon Shugaban Kasar Faransa Ya Ziyarci Kasar Ivory Coast
Tsohon shugaban kasar Faransa Nikolas Sercozy yana ziyar a kasar Ivory Coast.
Tsohon shugaban kasar Faransa Nikolas Sercozy yana ziyar a kasar Ivory Coast. Tashar Television France 24 ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya gana da shugaban Alhassan Watara inda ya jajanta masa kan hare haren ta'addancin da aka kai kan wasu wuraren shakatawa a kasar wanda ya kai ga kissan wasu mutane daga cikinsu har da na kasashen turai, 4 daga cikinsu yan kasar Faransa ne. Har'ila yau Jami'an tsaron na musamman guda ukku da kuma ukku daga cikin yan ta'adda hudu da suka kai wadan nan hare hare suma sun rasa rayukansu. Kafin haka dai ministan harkokin wajen kasar ta Faransa Jene Marck Aroo da kuma Barno Coznoove ministan harkokin cikin gida na kasar suka isa kasar Ivory Coasr a ranar Talata inda suka jajantawa yan kasar Faransa mazauna kasar Ivory coast inda kuma suka bayyana anniyar gwamnatin kasar Faransa na tallafawa ayyukan bincike kan lamarin