An Shiga Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A Rasha
https://parstoday.ir/ha/news/world-i26457-an_shiga_yakin_neman_zaben_shugaban_kasa_a_rasha
A Rasha yau Litinin aka shiga yakin neman zaben shugaban kasar dake tafe a hukumance.
(last modified 2018-08-22T07:01:09+00:00 )
Dec 18, 2017 07:33 UTC
  • An Shiga Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A Rasha

A Rasha yau Litinin aka shiga yakin neman zaben shugaban kasar dake tafe a hukumance.

A ranar 18 ga watan Maris na shekara 2018 za'a gudanar da zaben wanda shugaba mai ci Vladimir Putin ke sake takara a wani wa'adi na hudu.

A shekara 2000 ne Mista Putin ya fara shugabancin kasar, wanda idan har ya yi nasara a zaben hakan zai ba shi damar ci gaba da shugabancin wannan kasa har zuwa 2024.

Idan haka ta kasance Putin zai kasance wani shugaban kasar Rasha mafi dadewa kan karagar mulki tun bayan Joseph Staline.

Kawo yanzu jam'iyun siyasa 23 ne suka bayyana aniyarsu ta shiga zaben.