'Yan Jarida 65 Aka Kashe A Cikin Shekara 2017_ RSF
Dec 19, 2017 07:36 UTC
Wani rahoto da kungiyar kare hakin 'yan jarida ta duniya wato Reporters without Borders (RSF) ta fitar, ya nuna cewa 'yan jarida 65 ne suka gamu da ajalinsu a kan aiki a cikin shekara nan ta 2017.
Rahoton ya nuna cewa kisan 'yan jarida ya rage idan aka kwatanta da shekaru 14 da suka gabata.
Kamar dai irin wannan rahoton na bara kasar Siriya ce sahun gaba a inda 'yan jarida 12 suka rasa rayukansu akan aiki, sai kasar Mexico (11), Afganistan (9), Iraki (8) sai Philippines (4).
A shekara 2016 data gabata 'yan jarida 79 ne suka gamu da ajalinsu a kan aiki, kwatancin ragowar 'yan jarida biyar.