Barazanar Shugaban Amurka kan MDD Game Da Birnin Qudus
A yayin da MDD ke shirin yin zama domin tattauna kudurin da Shugaban Amurka ya dauka na ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin Isra'ila, wakiliyar Amurka a Majalisar ta yi kasashen Duniya barazana.
Wani sabon abu a tarihin Majalisar dinkin Duniya, wakiliyar Amurka a MDD Nikki Haley, ta gargadi mambobin kungiyar a kan cewa shugaba Trump, ya shaida mata cewa ta bayar da rahoto a kan duk wata kasa da ta juyawa Amurka baya a kan matakin da ta dauka na ayyana birnin Qudus a matsayin hedkwatar HKI a taron majalisar da za a yi inda za a kada kuri'a kan batun birnin Kudus a yau Alhamis.
A cikin wani jawabi da ya gabatar, Shugaban na Amurka, ya ce " Naji dadin sakon da Nikki ta isar a Majalisar Dinkin Duniya ga dukkan kasashen da suke karbar taimakon miliyoyin kudin Amurka, amma kuma su ka kada kuri'ar da za ta yi wa ra'ayinu yankan baya. Suna karbar kudinmu sannan kuma suna kin zabar mu, muna kallon irin wadannan kasashe, Su je kada su zabe mu, mu gaba ta kai mu domin zamu samu damar adana makudan kudade, kuma mu zamu taimaka musu ba.
A wannan Alhamis ne, kasashe mambobin majalisar dinkin duniya 193, za su yi wani taron gaggawa a kan bukatar da kasashen Larabawa da na musulmai suka gabatar na soke matakin da shugaba Trump ya dauka a game da birnin Qudus, wannan bukata na zuwa ne bayan da kasar Amurka ta hau kujerar naki a kwamitin tsaro na MDD, ana sa ran mafi yawa daga cikin manbobin Majalisar za su goyin bayan matakin da manbobin kwamitin tsaro na Majalisar 14 suka dauka na rashin amincewa da matakin shugaban Amurkan.
A ranar Litinin da ta gabata, kwamitin tsaron MDD ta kada kuri'a a kan taftarin da kasar Masar ta gabatar na neman a yi watsi da matakin da shugaba Trump ya dauka na ayyana birnin Qudus a matsayin hedkwatar Isra'ila, kudirin da ya samu karbuwa inda har ma kawayen Amurka na Turai kamar Faransa da Birtaniya suka aminci da wannan kudiri, dukkanin manbobin kwamitin sun amince inda ban da kasar Amurka da ta yi amfani da karfin da take da shi na hawan kujerar naki, wanda hakan ya sanya kudirin ba samu amincewa ba.
Saktare janar na MDD Antonio Guterres ya ce makomar birnin Qudus zai kasance ne bisa kudirin da kwamitin tsaro da na zauren Majalisar suka dauka
Ganin cewa kasar Amurkan ta koma saniyar ware a game da wannan kudiri, shi ya sanya Shugaban na Amurka ya billo da wannan mataki na barazana, domin tsoratar da wasu kasashe su goyawa matakin na sa baya, ko da yake a tsahon shekaru 70 na rayuwar MDD, kasar Amurka na amfani da irin wataki na barazana a bayan fage, wanda hakan ke tasiri ga wasu kasashe da suka kwallafa da taimakon MDD. to saidai wannan shi ne irin na farko da kasar ta fito bainar jama'a tayi wannan barazana.
Idan kuma zaman na yau yayi watsi da matakin na Amurka, hakan na zama babban koma baya ga sauren mutuncin da ya ragewa Amurka a idan Duniya.