Shugaban Peru Yayi Afuwa Wa Tsohon Shugaban Kasar Alberto Fujimori
Shugaban kasar Peru, Pedro Pablo Kuczynski, ya sanar da yin afuwa ga tsohon shugaban kasar Alberto Fujimori saboda dalilai na 'yan adamtaka saboda irin halin da tsohon shugaban yake ciki na rashin lafiya.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayyana cewar shugaban kasar Peru, cikin sakon ranar Kirsimeti ya sanar da yin afuwa wa tsohon shugaban kasar Alberto Fujimori wanda yake tsare a gidan yari bayan hukuncin da aka yanke masa na zaman gidan maza na shekaru 25 a shekara ta 2009 saboda hannun da yake da shi wajen kisan gillan da kuma rashawa da cin hanci.
Tun dai bayan wannan sanarwar, masu adawa da gwamnatin shugaba Kuczynski din suke ta sukarsa saboda afuwan da yayi wa tsohon shugaban, suna masu cewa yayi hakan ne kawai saboda wata manufa ta siyasa, saboda daya daga cikin sharadin da magoya bayan tsohon shugaban Fujimorin na majalisar kasar suka kafa masa na goyon bayansa a kokarin da ake yi na tsige shi a kwanakin baya shi ne yin afuwa wa tsohon shugaban.
A shekaran jiya asabar ne dai aka garzaya da tsohon shugaba Fujimorin, wanda ya shugabacin kasar Peru din tun daga shekarar 1990 zuwa 2000, asibiti sakamakon tabarbarewa yanayin lafiyarsa bayan shafe shekaru a gidan yari.